IQNA

A lokacin da yake taya murnar bikin babbar Sallah, shugaban  Amurka ya jaddada yaki da kyamar Musulunci

19:14 - June 17, 2024
Lambar Labari: 3491355
IQNA - A jawabin da ya yi na bikin Eid al-Adha, shugaban na Amurka ya yi ikirarin aniyarsa ta yaki da kyamar addinin Islama da kuma aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin kasashen biyu dangane da batun Falasdinu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Ain cewa, jawabin da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi wa al’ummar musulmi a yayin bukukuwan Sallah na kunshe da sakonni da dama.

A cikin wannan jawabin ya yi fatan alheri ga musulmi tare da bayyana cewa ya kuduri aniyar yaki da kyamar Musulunci da aiwatar da tsarin samar da kasashe biyu a Palastinu.

A cikin jawabin nasa wanda fadar White House ta fitar, ya ce: Ni da Jill muna taya Musulman Amurka da Musulman duniya murnar zagayowar ranar Sallah.

Biden ya kara da cewa: Kusan musulmi miliyan biyu daga sassan duniya ne za su halarci aikin Hajjin bana. Wannan tafiya ce mai tsarki wacce ta tattaro al'ummar musulmi daga kowane bangare na rayuwa muna musu fatan Alheri.

A wani bangare na jawabin nasa, shugaban na Amurka ya yi ikirarin cewa an kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, ciki har da dubban yara. An tilastawa iyalai barin gidajensu kuma gwamnatita tana yin duk abin da za ta iya don kawo karshen yakin, sakin duk wadanda aka yi garkuwa da su, ba da agajin jin kai da kuma yin aiki don samar da tsarin kasa biyu.

Ya nanata cewa: Har yanzu ina ganin cewa, samar da kasashen biyu ita ce hanya daya tilo ta samar da zaman lafiya mai dorewa ga Palasdinawa da Isra'ila, da kawo karshen tashin hankalin da ake yi a Gaza, da kuma kawo karshen yakin.

Ya kara da cewa: Na jajirce wajen tunkarar masu kallon kyamar Musulunci a Amurka, babu inda Amurka ke nuna kyama ga Musulman Amurka da Larabawa da suka hada da Falasdinu da sauransu.

Biden ya yi iƙirarin: Gwamnatina tana ƙoƙarin ƙirƙirar dabarun ƙasa don magance kyamar Islama.

 

 

4221960

 

 

captcha